Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya dawo da shirin inganta kula da masu fama da cutar kanjamau a Najeriya da ake kira ‘National HIV Treatment and Prevention of mother to Child Transmission (PMTCT), domin cin ma burin 90-90-90.
Adewole yace burin 90-90-90 shine aga cewa kashi 90 bisa 100 na mutane sun san matsayin su game da cutar kanjamau sannan kashi 90 bisa 100 na samun magunguna da kulan da suke bukata a Najeriya.
Ya bayyana cewa dawo da wannan shirin zai taimaka wa kasar wajen yi wa fannin kula da masu cutar kanjamau tanajin da ya kamata.
‘‘Hakan zai taimaka wajen kawar da yawan dogaro da kasar ke yi wa tallafin da kungiyoyin kasashen waje ke kawo wa.
A karshe Adewole yace ya dawo da wannan shiri ne bayan da ya tattauna da wasu ma’aikatun kiwon lafiya na kasashen waje a kasar Afrika ta kudu game da hanyoyin shawo kan irin wadannan matsaloli.
Bayanai sun nuna cewa mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne ya fara wannan shiri na (National HIV Treatment and Prevention of mother to Child Transmission (PMTCT) inda a lokacin Najeriya ke iya kula da mutanen dake dauke da cutar kanjamau har 10,000 yadda ya kamata.
Discussion about this post