Bafulatani ya mutu sanadiyyar duka a wasan sharo a Jihar Jigawa

0

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar mutuwar wani matashin Bafulatani, bayan an yi masa duka a wasan sharo a kasuwar Kantoga, cikin Karamar Hukumar Birnin Kudu, a jihar Jigawa.

Kakakin Yada Labarai na rundunar, Abdul Jinjiri, ya shaida wa Premium Times cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, bayan da wani mai suna Abdullahi Ibrahim Takai ya kai musu rahoto.

Takai yace shaida wa ‘yan sanda cewa ya jagoranci tawagar wasu matasan Fulani daga Takai ta Jihar Kano, inda suka je kauyen Kantoga domin haartar wasan sharo, na al’adar su ta Fulani, inda a wurin wasan aka doki daya ya mutu.

“Wanda ya shigar da kara ya ce wasu matasan da ya je da su, Ruwaji Maikudi, Ibrahim Lawal da Huseini Adamu, wadanda ba su wuce shekaru 23 ba, sun shiga wasan sharo su da wasu Fulani da suka je daga jihar Bauchi.

“Abin takaici, Ruwaji ya shiga gasar duka shi da wani matashi mai suna Ibrahim Auwal daga jihar Bauchi, inda bayan ya ci duka, ya fadi somamme. An garzaya da shi asibiti, amma a can ya rasu a lokacin da ya ke karbar magani.

Jinjiri ya ce wanda ya yi dukan ya tsere, amma ‘yan sanda sun kama shugaban tawagar ta su daga Bauchi, mai suna Ibrahim Mohammed, dan shekara 56. Kuma ana ci gaba da bincike.

Wasan sharo ko shadi, wasa ne na matasan Fulani inda su ke wa junan su duka da tsabga, da nufin nuna jarumta a tsakanin su.

Share.

game da Author