Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kebbi (SEMA) Sani Dododo ya yi kira ga mutane da su rika kula da duk ababen da ka iya tada gobara musamman a yanzu da aka fara shiga yanayi na hunturu.
Dododo ya yi wannan kira ne ranar Juma’a yayin da ya ziyarci gidan wani malam Umar Argungu da iyalen sa gaba daya gobara ta lashe su.
Umar mazaunin karamar hukumar Arugungu ne sannan kuma shi ma’aikaci ne a masana’antar sarrafa auduga ‘West African Cotton Company Limited (WACCOT)’ dake jihar.
Dododo ya bayyana cewa Umar ya tafi wajen aiki ne a daren ranar Alhamis inda washe gari daya dawo gida sai ya taras gobara ta lashe iyalen sa kaf.
An dai gano cewa matar Umar ta manta na’urar dafa ruwa ne wato hita a kunne a lokacin da za su yi barci.
Gaba daya ‘ya’yan Umar 3 da matar sa har da wata yar makwabta sun kone kurmus a gobarar.
Discussion about this post