Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilan da suka sa ba za ta iya biya wa ma’aikata bukatun su na yin karin mafi kankantar albashi zuwa naira 30,000 ba.
Kungiyoyin Kwadago na NLC, TUC da kuma ULC sun sha alwashin fara yajin aiki na kasa baki daya a gobe Talala, muddin gwamnatin tarayya ta ki biya musu bukatun su.
Gamayyar kungiyoyin dai sun zargi gwamnati da karya alkawarin da ta dauka na biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, a wani taron cimma matsaya da suka yi tsakanin shugabannin kwadago, gwamnati da kuma masu kamfanonin da ba na gwamnati ba.
Sai dai kuma a na ta bangaren, gwamnati ta ce ba su yi wannan zaman cimma yarjejeniyar ba. Kuma sai ita gwamnatin ta tsaya cewa naira 24,000 kadai za ta iya biya, yayin da su kuma gwamnonin jihohi suka tsaya cewa naira 22,500 za su iya biya.
Jiya Lahadi kuma kungiyoyin kwadago sun bijire wa gayyatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya ya yi masu domin a yi zaman sulhun neman hana su tafiya yajin aiki.
DALILIN KASA BIYAN NAIRA 30,000
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce damuwar gwamnatin tarayya ba wai jin dadin ma’aikatan kasar nan ne abubuwan da ke kan ta ba kadai ba, akwai sauran abubuwan da za a yi la’akari da su domin za su shafi tattalin arzikin kasa
Akwai kuma batun yadda ko da an yi karin albashin, to darewar biyan ma abin dubawa ne, domin akwai jihohi da dama wadanda su naira 18,000 da ake biya a yanzu ma sai da gumin goshi suke iya biya, wasu kuma ba su ma iya biyan hakan.
Ya yi nuni da cewa jihohi 27 a halin yanzu su na shan wahala wajen biyan naira 18,000 da ake biya a halin yanzu, wadda kungiyar kwadago ta raina, ta ke neman kari.
DALILIN KIN ZUWAN MU GANAWA DA SAKATAREN GWAMNATI -NLC
A ranar Lahadi, Babban Sakatare na Kungiyar Kwadago ta Kasa, Peter 0zo-Esan, ya shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa su na da dalilin kin halartar taro da Sakataren Gwamnatin Tarayya.
“Ba mu da wani labarin akwai wani taro da Sakataren Gwamanatin Tarayya. Gwamnatin da ta garzaya kotu ta kai mu kara, aka ba yanke cewa haramta mana tafiya yajin aiki, kuma ba ta sanar da mu batun zuwa kotu ba, sai dai a jarida mu ka ji, to ba ta da kwarjinin da za mu sake zama teburi daya da ita.
“Ko ma da a ce mu na da masaniyar ganawar, to ba mu da bukatar halarta balle ma mu zauna da gwamnatin. Mu taron da mu ke da masaniya da shi, wanda kuma za mu halarta, shi ne taron bangarori uku a Abuja ranar Litinin.”Inji shi.
Discussion about this post