Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wani mai auren ‘yar sa mukamin Shugaban Hukumar Raya Al’umma Mazauna Kan Iyakar Kasa a asirce.
An nada Junaid Abdullahi a ranar 18 Ga Oktoba, amma a asirce, ba tare da an yi sanarwa ba.
Abdullahi shi ne mijin Zulaihat, ‘yar Buhari ta farko wadda ta rasu cikin 2012 bayan ta sha fama da nakuda a wurin haihuwa.
Ta rasu ta na da shekaru 40.
Abdullahi ya karbi ragamar shugabancin hukumar ne daga hannun Jummai Idako.
Irin wannan nadi da aka yi masa, an saba jin an yi sanarwa ne a fadar shugaban kasa ko kuma ofishin sakataren gwamnatin tarayya.
Sai dai kuma ba a san dalilin da ya sa bangarorin gwamnatin biyu suka yi gum da bakin su ba.
Amma wata majiya wadda tun da farko ta ke da masaniyar nada Junaid, ta ce mai yiwuwa an ki bayyana ba shi mukamin a sarari ne, don gudun kada a kara sukar Buhari da laifin nuna kabilanci ko banganranci a wajen nade-naden mukamai da ya ke yi.