Dana takarar shugaban kasa, a karkashin jam’iyyar PT, watau Peoples Trust, Gbenga Olawepo-Hashim, ya caccaki jam’iyya mai mulki, APC dangane da yadda ta haddasa wa miliyoyin ‘yan Najeriya fatara da talauci.
Cikin wata takardar manema labarai da ya aiko wa PREMIUM TIMES a jiya Lahadi, ya ce APC ta gaza tunanin da aka yi mata har aka zabe ta. Maimakon ta samar wa al’umma arziki da yalwa, Hashim ya ce mutane milyan 88 na cikin kuncin talauci da fatara, sanadiyyar tukin ganganci da gwamnatin APC ke yi wa Najeriya.
Ya ce a cikin watanni hudu da suka gabata zuwa yau, mutane miliyan 1.1 suka afka cikin kangin fatara, ga kuma dan Karen tsadar man fetur da gwamnati Buhari ta kara wa farashi.
Hashim ya ce gwamnatin APC ba ta iya tafiyar da tattalin arziki yadda zai kara samar da yalwa a cikin kasa ba, kuma ba ta da wani ingantaccen tsari, kawai bara-da-ka gwamnatin ke tafiya, a cikin duhu.
Hashim ya kara da cewa bayanin kididdigar da Cibiyar Brooklyn ta fitar cewa ‘yan Najeriya miliyan 88 na cikin fatara, abin firgitarwa ne matuka.
Ya kuma nuna rashin jin dadin yadda matasa masu rasa aikin yi ke ta kara yawa a kasar nan.
Dan takarar shugaban kasar ya yi nuni da halin da kasar nan ka iya shiga nan gaba idan gwamnatin Buhari ta ci gaba da ramto makudan kudade ido rufe, domin babu wani tsarin da gwamnatin ke yi wajen samun wasu kudaden shigar da za a iya biyan bashin da su nan gaba, har yanzu dai da kudaden man fetur ta dogara.