A yau Laraba ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Tyopev Terna ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani dan sanda a kwanar Soja dake karamar hukumar Jos ta Arewa.
Terna ya fadi haka ne wa manema labarai a garin Jos sannan yace ‘yan bindigan sun kashe Abullahi S wanda ke aiki da rundunar ‘Operation Safe Haven da karfe 7:50 na yammacin Talata.
” Abdullahi ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da ya je taimakawa wata yarinyar da wadannan ‘yan bindiga suka sace cikin wannan dare.
Ya ce sun sami masaniyar haka ne a lokacin da wani magidanci mai suna Alhaji Idris Gambo ya kawo musu karar cewa wasu ‘yan bindiga sun sace ‘yar sa mai suna Hafsat Gambo mai shekaru 21 daga gidan sa dake kwanar Soja.
” Da jin haka sai muka bazama muka nufi gidan Idris inda muka iske Abdullahi rai a hanun Allah.
‘‘Bayan mun kai shi asibitin Bingham dake garin Jos ne Abdullahi yace ga garin ku nan.”
Terna ya ce sun fara gudanar da bincike domin taso keyan mutanen da suka aikata haka.