Mutane 11 sun kone a dalilin fashewar tukunyar iskar gas a Abuja

0

Wani abin tashin hankali da ya faru a babban birnin tarayya Abuja ranar litinin, shine fashewar tukunyar iskar gas a wani gidan cin abinci.

Gidan cin abincin mai suna Rosy Resturant’ ta kama da wuta ne inda ma’aikata uku da kwastamomi tara suka kone.

” Na kone a hannu da fuska ne amma da ya ke ina da ciki, na fi ji da dan dake ciki na.” Inji ma’aikaciyar gidan abincin mai suna Ajayi.

Bayanai sun nuna cewa mafi yawan mutanen da suka sami rauni sun kone a hannayen su ne da fuskokin su. ” Yanzu haka suna asibiti ana kula da su.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Abuja (HHSS) Aminu Mile ya bayyana cewa hukumar za ta gudanar da bincike domin gano musabbabin abin da ya faru.

Share.

game da Author