Ma’aikatan hukumar kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta tsige shugaban ta Yusuf Usman

0

Kungiyar ma’aikatan hukumar inshoran kiwon lafiya ta kasa (NHIS) sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta sauke shugaban hukumar Usman Yusuf daga aiki bisa zargin wawushe kudaden hukumar da rashin gudanar da aiyukka yadda ya kamata.

Jami’in kungiyar Isaac Ojemhenke ya sanar da haka wa manema labarai a Abuja inda ya kara da cewa wannan shine karo na biyu da ake zargin Yusuf da aikata laifuka irin haka a hukumar.

Ojemhenke ya bayana cewa Yusuf ya yi amfani da kudaden hukumar da ya kai Naira miliyan 3.6 domin zuba man fetur a wasu motocin sa a lokacin da aka dakatar da shi .

Sannan yace Yusuf ya dauki naira miliyan 17.5 da aka ware domin horas da ma’aikatan hukumar ya bada su kwangila wa kamfanin wani dan uwansa mai suna Hassan Kabir a maimakon horas da ma’aikatan.

” Har Yanzu dai muna nan muna sauraron bayanin dalilin da ya sa Yusuf yin amfani da N46,798,512.00 domin tafiyar sa zuwa kasar Netherlands da kuma yin amfani da Naira biliyan 25 da wai ya saka jari dasu.

Ojemhenke ya ce Yusuf na wasu aikiyan da zai raba kan ma’aikata a hukumar.

A dalilin haka ne kungiyar ke kira ga gwamnati da ta sauke Yusuf daga kujeran aikinsa domin hakan ya zama abin koyi wa sauran ma’aikata.

Idan ba a manta ba a kwanakin bayan ne mininstan kiwon lafiya Isaac Adewole ya dakatar da Yusuf daga aikinsa a dalilin zargin wasushe kudaden hukumar da rashin gudanar da aiyukka yadda ya kamata a hukumar.

A karshe shugaban kwamitin kula da aiyukan hukumar inshoran kiwon lafiya Ifenne Enyanatu ta bayyana cewa ta saurari kararrakin aiyukan Yusuf da kungiyar ma’aikatan ta shigar a ofishin su, Sannan ta ce kwamitin za ta zauna daga ranar 17 zuwa 18 ga watan Oktoba domin tattauna duk laifukan da ake zargi Yusuf da su.

Share.

game da Author