Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa zuwa yanzu ta yi wa mutane akalla 377,000 allurar rigakafi cutar Kwalara a jihar Adamawa.
WHO ta bayyana haka a wani rahoto da ta fitar a karshen makon da ya gabata a garin Yola.
Idan ba a manta ba a watan Mayu ne cutar kwalara ta bullo a kananan hukumomin Mubi ta Arewa, Mubi ta Kudu da Maiha a inda mutane da dama suka kamu da cutar.
WHO ta kuma gina asibitocin kula da mutanen da suka kamu da cutar na gaggawa a wannan lokacin kuma hakan ya san an samu ragowar wadanda suke fama da cutar da mace mace da aka yi ta fama dashi matuka.
” A wannan lokacin da cutar ta bullo a jihar WHO ta dauki ma’aikata 35 wanda ta biya daga aljuhunta domin inganta kula da mutanen da suka kamu da wannan cuta. Sannan ta samar da duk magungunan da aka yi amfani da su wajen kula da mutanen da suka kamu da cutar tare da wayar da kan mutane game da tsaftace muhalinsu da abincin su domin guje wa kamuwa da cutar kwalara’’.
A yanzu haka WHO na horas da zababun ‘Yan jarida da aka zabo daga jihohin Adamawa,Yobe da Barno domin a koya musu makaman aiki kan yadda za su rika dauko rahotanni yadda ya kamata musamman ya yankunan Gabashin Arewacin Najeriya.