Akwai yiwuwar Mal Salihu Sagir Takai ya lashe gwamnan Kano a 2019, Daga Adam Muhammad

0

A ranar Asabar din da ta gabata ne miliyoyin jama’ar jihar Kano Masoya Dan takarar gwamnan Kano a karkashin tutar jam’iyyar PDP wato Mallam Salihu Sagir Takai suka yi fitar Dango domin tarbo shi daga filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, wanda taron ya samu tagomashi na sama da mutum milliyan uku suka yo tattaki domin nuna goyon bayan takarar da uwar jam’iyya ta kasa ta sahale masa.

Taron yayi armashi duk da cewa an sanar da mutane a kankanin lokaci.

Wannan ya nuna cewa Jama’ar jihar kano sun karbi wannan takara hannu biyu biyu kuma sun amince za su kada masa kuri’a a zabe mai zuwa.

Daga karshe muna godiya ga jagororin jam’iyyar PDP a matakin kasa da jihar baki daya. Godiya ta musamman ga Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP wato Alhaji Atiku Abubakar da sauran yan takarkaru a matakin Gwamna da sauran kujeru da dukkan al’ummar jihar kano da suka bada lokacin su da dukiyoyin su wurin wannan tarya.

Share.

game da Author