Kungiyar likitocin Najeriya (NMA) ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kafa hukumar MCDN, wato hukumar da zai rika kula da ayyukan likitocin Najeriya.
NMA ta ce fannin kiwon lafiya ta yi shekaru uku kenan cif da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ruguje tsohuwar hukumar batare da ta kafa wata sabuwa ba.
” Sanin kowa ne cewa hukumar MDCN hukuma ce dake kula da al’amarorin aiyukkan likitoci domin tabbatar cewa mutanen kasar nan na samun ingantacciyar kiwon lafiya amma tun da gwamnati ta rusa hukumar ta ki yin komai a kai.
” A dalilin haka muna so mu sanar wa ‘yan Najeriya cewa idan har aka ga ana samun matsala a fannin kiwon lafiya, su zama shaidan mu cewa matsalar ba daga wurin mu bane.