Wani abin al’ajibi da ban tsoro ya auku a kauyen Iloro-Ekiti dake karamar hukumar Ijero jihar Ekiti inda shanu 23 suka mutu a dalilin tsawa da ya fado a kan su.
Makiyayin dake kiwon wadannan shanun Abdulkadir Kadiri ya ce tun da yake bai taba gain irin wannan abu ba sannan ya ce ya rungumi kaddara game da abin da ya same shi.
” Ni dai na san babu wani da ke bibiya ta da sharri a ballantana in ce wai an far mini da.” Inji Kadiri.
Mai unguwar wannan kauye Joseph Alofe ya tabbatar da aukuwar wannan abin alajabi sannan ya kara da cewa makiyayin muutum ne dake son zaman lafiya a duk inda yake.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran attajiran jihar da su agaza wa wannan makiayayi bisa ga wannan rashi da yayi na dukiyar sa.