Kotu ta dakatar da jam’iyyar APC daga gudanar da zaben fidda gwanin Sanata na Kaduna ta Tsakiya

0

Kotu a jihar Kaduna ta dakatar da jam’iyyar APC daga gudanar da zaben fidda gwani na shiyyar Kaduna ta tsakiya a bisa kara da mai taimaka wa gwamnan jiha Uba Sani ya shirgar gabanta cewa an tauye masa hakki na kin amincewa yayi takarar kujeran sanata na yankin.

Idan ba a manta ba, a jiya ne jam’iyyar APC ta kasa ta fitar da sunayen wadanda ta amince su yi takarar sanata a jihohin kasar nan. Sai dai kuma a jihar Kaduna dan takara daya ne tal a aka amince wa ya yi takarar fidda gwanin cikin yan takara hudu da suka sayi fom.

Sanata Shehu Sani ne kadai jam’iyyar ta amince da yayi takarar kujerar sanata na Kaduna ta tsakiya.

Tun bayan fidda wanna jerin sunaye, magoya bayan jam’iyyar APC a jihar suka fusata inda shugaban jam’iyyar na yankin Kaduna ta tsakiya Aminu Jibo ya bayyana cewa ba za su amince da wannan shiri ko kuma tsari na uwar jam’iyyar ba.

” Jam’iyyar bata yi wa wadannan ‘yan takara adalci ba kuma muna kira ga jam’iyyar da ta gaggauta yin gyara ko kuma mu dauki mataki kai tsaye game da haka.

” Ba zai yiwu ace wai wadanda suka nemi gurgunta tafiyar jam’iyyar a jiha ne za a nada da karfin tsiya sannan kuma ace an yi wa jam’iyya adalci. Ba za mu amince da haka ba.” Inji jibo

Lauyan mai ba gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkar siyasa, Uba Sani, Sule Shuaibu ya shigar da kara babban kotu dake Kaduna inda kotu ta yanke hukuncin dakatar da uwar jam’iyyar daga gudanar da zaben fidda dan takara na kujerar sanata na yankin Kaduna ta tsakiya.

Kotu ta umarci hukumar Zabe, Sanata Shehu Sani da shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole da a koma yadda tsarin yake kafin 2 ga watan Oktoba, ke nan tun kafin a cire sunan Uba Sani daga cikin ‘yan takarar kujeran sanata.

Lauyan Uba Sani ya bayyana wa kotu cewa tun a lokacin da Uba Sani ya ji kishin-kishin din za a cire sunan sa ya rubuta wa shugaban jam’iyyar APC wasika cewa kada a kuskura ayi haka. Cewa ya cika dukkan sharuddan da ake bukata na yin takarar kujerar sanata, bai ga dalilin da zai sa a zame sunan sa daga cikin jerin wadanda za su yi takara ba.

Za a ci gaba da wannan shari’a ne ranar 15 ga watan Oktoba.

Share.

game da Author