Najeriya za ta hada hannu da kasar Britaniya domin hana yaduwar cututtuka

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya da hukumar kula da kiwon lafiya ta Britaniya (PHE) sun amince su saka hannu a wata takardar yarjejeniyya domin hana yaduwar cututtuka.

Bayanai sun nuna cewa Britaniya ta saka hannu a yarjejeniyar ne tare da wasu kasashen Afrika hudu sannan ta ware yuro miliyan 16 don ganin an dakile yaduwar cututtuka daga wata kasar zuwa wata.

Najeriya da Britaniya sun amince da haka ne bayan gano wasu mutane biyo da suka taso daga Najeriya zuwa kasar Britaniya na dauke da cutar ‘Monkey Pox.

Jakadan kasar Britaniya zuwa Najeriya Paul Arkwright ya bayyan cewa hada guiwar da Najeriya ta yi da Britaniya zai samar wa fannin kiwon lafiya na kaaar mafita nagari.

” Za mu tabbatar duk wata dabarar bincike, gano cututtuka, hanyoyin kawar da cututtuka da muka sani irin ta zamani za mu koya wa Najeriya.

Share.

game da Author