Sanata Shehu Sani ya koma jam’iyyar PRP

0

Sanatan dake wakiltan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana sabuwar jam’iyyar da ya koma.

Shehu Sani ya ce ya koma jam’iyyar PRP ne ganin cewa ita ce ke tattare da irin munufofin adalci kishin talaka wanda shine burin sa a siyasan ce.

Shehu ya kara da cewa gara ya rufa wa kansa asiri ya tsira da mutuncin sa ko da a akulki ne da ya ci gaba da zama a dankareren gidan da ba ta da kima ko daraja a idanun mutane.

Shugaban jam’iyyar PRP na jihar Kaduna, Mataimaki Tom Maiyashi, ya tabbatar da dawowar Sanata Shehu Sani jam’iyyar PRP cewa tuni har ya amshi katin zama dan jam’iyyar a mazabar sa na Tudun Wada.

Idan ba a manta ba ranar Asabar din da ta gabata ne Sanata Shehu Sani ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC.

Jam’iyyar APC ta musanya sunan Shehu Sani da ta ba tikitin kujerar takarar sanata na Kaduna ta Tsakiya da Uba Sani.

Shehu Sani ya bayyana cewa tunda abin ya zama haka, ya hakura da ci gaba da zama dan jam’iyyar APC daga wannan rana.

Idan ba a manta ba, sanata Shehu Sani da gwamnan jihar Kaduna sun saka kafar wando daya ne tun bayan da aka kafa gwamnati a 2015.

Tun daga wancan lokacin aka yi ta kai ruwa rana a tsakanin su inda har ya kai ga jam’iyyar a jihar Kaduna ta kori sanata Shehu Sani.

Sai dai kuma zuwan Oshiomhole, shugaban jam’iyyar APC sai dankon zumunci ya karfafa a tsakanin Shehu Sani da jam’iyyar a sama in da tuni aka yi sanata nadin dan gata.

Yanzu dai ya tabbata Uba Sani ne dan takarar Sanata na Kaduna ta tsakiya shikuma Shehu Sani ya tattara-na-shi- ina-shi ya fice daga jam’iyyar

Share.

game da Author