Wata rana cikin shekarun 1990, Pat Isaac, wanda ma’aikacin kamfanin Nigeria Airways ne, ya hau saman rufin da tankin ruwan ofishin su ke a kai, da nufin duba ruwan da ke ciki. Dama kuma a bangaren kula da ruwa Isaac ke aiki.
Sai dai kuma a ranar yay i rashin sa’a, ibtila’i ya fada masa, yayin da dirkokin da aka dora tankin ruwan suka karye, Isaac ya rikito kasa. Tun daga ranar ya rasa inda ya ke, kuma wuyan sa lauye, fuskar sa ta rika kallon baya.
Ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya shafe watanni da dama kan sa a jirkice, ya sha fama da jiyya a asibiti ta tsawon watanni da dama. Ya ce jama’a da dama sun dauka ba zai rayu ba.
Isaac ya ce bayan shekaru kadan da yin hatsarin, sai kawai ya yi ritaya, amma tun daga lokacin da ya bar aiki bai taba samu kudin fansho ko na sallama daga aiki ba. Sai fa cikin watan Oktoba din nan da mu ke ciki.
Ya ce sun yi jiran-gawon-shanu na tsawon lokaci, wasu abokan aikin su sun mutu, wasu sun gurgunce, wasu kuma tsufa da fatara da talauci sun rafkar da su, ko fita ba su iya yi.
“Amma cikin ikon Allah wannan gwamnatin ta tuna da mu.”
Ba Isaac kadai ba ne ya samu matsalar tawayar jiki ko ta rayuwa ba daga cikin tsoffin ma’aikatan kamfanin sufurin jirage na Nigeria Airways. Da yawa daga cikin su da PREMIUM TIMES ta tattauna da su, sun bayyana mata irin rayuwar kunchi da fatara da talaucin da suka shiga bayan durkushewar kamfanin jiragen da kuma ritayar da suka yi, saboda rashin biyan su hakkokinn su.
Alimi Kuye cewa ya yi ya san abokan aikin sa guda biyar da suka mutu saboda kasa biya wa kan su kudaden maganin ciwon da ya kwantar da su.
Shi kuwa Adigun, sakin bakin sa ya yi inda ya rika zabga tsinuwa da ashariya a kan gwamnatocin da suka shude, wadanda suka hana su hakkokin su.
“Gwamnatin da muka yi wa aiki a lokacin da muke da karfi, ta yi watsi da mu, ta bar mu cikin kunci, wasu sun mutu wasu sun samu nakasa. Amma ga shi yanzu bayan mun tsufa an samu gwamnatin da ta dube mu da idon rahama ta biya mu hakkokin mu.”
An kafa Nigeria Airways cikin 1958, ya kakare a cikin 2003, a lokacin mulkin Ousegun Obasanjo.
Gwamnatin Umaru Yar’Adua ta biya wasu ma’aikatan hakkokin su, amma da Goodluck Jonathan ya hau mulki, ba a ci gaba da biya ba.
Cikin makon jiya ne gwamnatin tarayya ta fara tantance biyan tsoffin ma’aikatan a karkashin sa-idon hukumomin EFCC da ICPC.
Sai dai kuma an kara sati daya daga ranar 22 Ga Oktoba da aka ce za a daina aikin tantancewar, saboda ana cin karo da ‘yar tangarda.
Tsoffin ma’aikatan su na shan wahala sosai kafin a tantance su. Kamar yadda a Lagos wani ya fada wa PREMIUM TIMES cewa shi mazaunin Igando ne cikin Karamar Hukumar Alimosho.
“Garin mu da nisa. Idan dai har ban samu EFCC ta tantance ni a yau har ta ba ni katin tantancewa ba, to a gaskiya a nan zan kwana.”
Ya ce da yawan wadanda suka je wurin tantancewar daga wurare masu nisa, a wurin suka kwana, wasu kuma a can din za su sake kwana.
Ya ce idan mutum ma ya tafi gida, to cinkoson motoci da safe ba zai bari ya koma wurin tantancewar da wuri ba.
“Zuwa da komawa gida zan bukaci naira dubu daya a kullum. To ina zan samu wannan kudin a kullum? Ai gara na kwana a nan kawai.
Ya ce a layi shi ne na 184, abokin sa kuma na 271.
Masu irin wannan matsalar suna da yawa, domin saboda yadda ake kwana da yini a wurin tantancewar, har ta kai masu kananan sana’o’i sun kafa ‘yan rufunan saida abinci, ruwa, lemun kwalba da kayan bukatu na yau da kullum.
Bayan su kuma akwai dandazon masu na’urar gurza takardun da ake kira photocopy su na cin kasuwar su a wurin.
Kunle Ajayin na cikin wadanda suka kammala tantance su, kuma ya gode wa gwamnatin Yar’Adua da ta Muhammadu Buhari. Yadda ya ke magana a cikin fara’a da annashuwa, tamkar ma kudaden sa sun rigaya sun shiga aljihu ko asusun ajiyar sa na banki.