Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa dole ne fa gwamnati ta maida hankali wajen ganin an kawar da cutar shan-inna a kasar nan.
Osinbajo ya fadi haka ne a zama da ya yi da gwamnonin jihohin kasar nan da ma’aikatan kawar da cutar shan inna a Abuja a makon da ya gabata.
Osinbajo ya koka bisa ci baya da ake samu wajen aikin kawar da cutar a kasar nan.
Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne tsohuwar ministan Kudi ta kasa, Kemi Adeosun ta bayyana cewa gwamnati ta ciwo bashin dala miliyan 150 don ganin an kau da wannan cuta a kasar nan.
A dan kwanakinnan ma an samu rahoton bullowar cutar a jihar Bauchi.
” A karamar hukumar Bauchi kashi 52 bisa 100 na yara ne aka yi wa allurar rigakafin gaba daya, kashi 29 bisa 100 ba a yi wa allurar gaba daba ba, 19 bisa 100 kuwa ba ayi musu allurar ba ma.
Osinbajo ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a Najeriya, da gwamnonin jihohi da su hada karfi da karfe don ganin an samu nasarar kau da wannan cuta kwata-kwata.