RIKICI: Buhari ya tafi taron ganawa da shugabannin addinai a Kaduna

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Kaduna domin taron ganawa da shugabannin addinai da sarakunan gargajiyar jihar.

Sabon rikici ya barke wanda ya haifar da kisan jama’a da dama, ciki har da Basarake Mai Daraja ta Daya, Maiwada Galadima na Masarautar Adara.

Ana zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe Galadima.

Rikicin farko na baya-bayan nan ya taso ne daga garin Kasuwan Magani, wanda akalla aka kashe mutane 55.

Rikicin ya watsu cikin garin Kaduna, inda a can ma a rana daya aka kashe mutane 22.

Wannan ne ya sa gwamnatin jihar saka dokar hana walwala ta awa 24, amma an sassabta dokar a ranar Lahadi da ta gabata.

Buhari ya tashi daga filin jirgi na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da misalin karfe 9:30 na safe.

Ana gudanar da taron ne a dandalin Murtala Square, inda za a gudanar da taron tare da Buhari.

Su ma sarakunan gargajiya da shugabannin addinai duk tuni sun kama wuri sun zauna.

Share.

game da Author