GARKUWA: ‘Yan sanda sun ceto matar shugaban Kwalejin Gona ta Zamfara

0

Rundunar ’Yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kubutar da Hindatu Ibrahim, matar Shugaban Kwalejin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Bakura a jihar Zamfara.

Matar mai shekaru 35 da haihuwa, an sace ta ne a ranar 27 Ga Oktoba, a cikin gidan su da ke cikin harabar kwalejin da dare.

An ceto ta ne kwana daya bayan da aka yi garkuwar da ita.

Kakakin Yada Labaran ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata takardar manema labarai da ya fitar, cewa wadanda suka yi garkuwar da ita, sun nausa da ita ne wani wurin da ba sani ba.

Ya ce nan da nan sai jami’an su suka fara amfani da dabarun fasahar gano inda aka boye ita Hindatu din.

Ya jaddada cewa ba a biya diyyar ko sisi ba kafin a sake ta.

Share.

game da Author