Sanata Bukar Abba, dan APC daga jihar Yobe, ya ragargaji salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari a cikin shekaru uku da suka gabata cewa, rashin tabuka abin kirkin da da bai yi ba a yankin Arewa maso Gabas, to sakayyar sa na nan ta na jiran sa a lokacin zaben 2019, cikin watan Fabrairu.
Jihohin Arewa maso Gabas sun hada da Yobe, Barno, Bauchi, Adamawa, Bauchi da Gombe.
BUHARI YA YI RATSE YA SAKI HANYA
Bukar Abba, wanda ya yi gwamnan jihar Yobe har sau uku a baya, ya bayyana cewa Buhari ya yi ratse, ya saki hanyar da aka yi tunani da alkawarin dauka a zaben 2015.
Ya ci gaba da cewa Buhari bai cancanci zabe a 2015 ba, kawai dai yankin su na Arewa maso Gabas ya samu kan sa cikin wani mawuyacin hali ne, shi ya sa suka yanke shawarar zaben Buhari.
GUGUWAR 2015 CE ZA TA KADA BUHARI A 2019
Yayin da yake jawabi a taron kaddamar da wani littafi a Abuja, Bukar ya ce, “Siyasa Arewa maso Gabas a ko da yaushe ta na shan bamban da ta Arewa maso Yamma, domin ain kowa ya san cewa a lokacin APC ne muka samu hadin kai a yankin a karo na farko. Saboda jama’a na tunanin cewa idan ya ci zabe abubuwa za su canja.
“Amma yanzu da muka kusanci zaben 2019, dole na yi kakkausan gargadin cewa abubuwa fa a yanzu ba kamar yadda suke a 2015 din da aka sani suke a yanzu ba.
Domin Buhari dai guguwa ce kawai ta fizge jama’a har suka zabe shi a 2015.
KO DA MAGUDI BA ZA A YI NASARA BA
“Na je na fadi, kuma na kara fadi a saukake, kuma kai tsaye cewa abubuwa fa ba su canja ba, sai ma kara shiga kuncin rayuwa da al’umma suka yi. Don haka kada ma mu yi tunanin cewa ko da tafka magudi za mu iya cin zabe.
“A kullum tattalin arziki sai kara tabarbarewa ya ke yi, saboda maimakon mu maida hankali wajen fuskantar gaba mu daina waiwayen baya, to sai mu ka buge wa waiwaye, komai ya faru maimakon a fito da hanyoyin warwarewa, sai a yi cirko-kirko ana dora laifin a gwamnatin da ta gabata.
Bukar ya yi wadannan kakkausan jawabai ne a wurin kaddamar da littafin sa mai suna “Poorlitics” a babban dakin taro na otal din Barcelona, Abuja.
Bukar wanda ya cika shekaru 70 a duniya a ranar da ya kaddamar da littafin sa, ya ce littafin nasa ya na magana ne a kan yadda za a dakile ragargazar kudi a lokacin siyasa ko neman zabe.
DA NAIRA DUBU 20 NA ZAMA GWAMNA
Sanata Abba Ibrahim ya bayyana cewa a lokacin da ya fito takarar gwamnan jihar Yobe a cikin 1991, naira 20,000 ce kacal a asusun ajiyar san a banki.
A lokacin ya yi gwamna tsakanin 1991 zuwa 1993. Sai kuma ya dawo ya sake yi daga 1999 zuwa 2007. Tun daga lokacin kuma ya ke sanata har zuwa yau, inda zai sauka a 2019.
KO BUHARI YA CANJA KO YANKIN AREWA MASO GABAS SU CANJA SHI
Sanatan ya yi nuni da cewa a yadda mulkin Buhari ke tafiya, ko kuma yadda shi Buhari din ke tafiyar da mulkin sa, to kamar bai dauki yankin Arewa maso Gabas da muhimmanci ba. Don haka ya ce tabbas idan jama’ar yankin ba su fara ganin wani ci gaba a rayuwar su a kasa ba, to ba su fa da wani zabi sai na canja Buhari kawai.
IDAN TA BACI ZAN CE KOWA YA ZABI WANDA YA KE SO
Bukar ya bayyana cewa zai zauna ya zuba ido daga nan zuwa lokacin da zaben 2019 zai zo a watan Fabrairu, idan ya ga Buhari ya yi wani gagarimin aikin ci gaban jama’a a yankin, to zai ce a zabi APC. Idan kuwa Buharib bai yi komai ba har zabe ya zo, to Bukar ya ce zai ce wa jama’a kowa ya san inda dare ya yi masa, ya zabar wa kan sa mafita kawai.
YAKI DA RASHAWA KO BI TA DA KULLI
Sanatan ya ce Buhari ba zai saisaitu ba har sai ya daina salon yaki da cin hancin da ya ke yi, wanda a cewar sa ba komai ba ne sai bi ta da kulli, kawai, domin akwai ‘yan lelen da ba a bincikar su.