RAHOTON MUSAMMAN: Sunayen Wadanda Suka Durkusar da ‘Nigeria Airways’ kuma suka narke cikin gwamnatin Buhari

0

Ranar Talatar da ta gabata ne Majalisar Tarayya ba ta yi wata-wata ba, ta gaggauta zartas da kwamitin binciken yadda aka durkusar da kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na ‘Nigeria Aiways’, wanda aka fara biyan kudaden fanshon tsoffin ma’aikatan kamfanin, mallakar Gwamnatin Tarayya.

Bayan an shafe makonni ana aikin tantance tsoffin ma’aikatan, an kididdige har mutane 6,000 da za a biya jimillar naira biliyan 45, wadanda ba a taba biyan su ko sisi ba, tun daga 2003, shekarar da kamfanin ya durkushe kasa warwas.

A can baya, gwamnatin Olusegun Obasanjo ta taba kafa kwamitin bincike a cikin 2002, a karkashin Mai Shari’a Obiora Nwazota, wanda ya gano cewa wasu mahandama sun wawure naira bilyan 60 na kamfanin.

Wancan kwamiti ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da jami’an ‘yan sanda ta kwato kudaden da aka wawure, daga hannun mahandan, kuma a gurfanar da su kotu, musamman tunda su na raye, ana ganin su a kasar nan sai fantamawa suke ta yi.

JERIN CARBIN ‘YAN HARKALLA

Cikin shekaru tamanoni, wato farkon 1980 zuwa 1985, Nigeria Airways ya mallaki jirage, 32. Amma ya zuwa 2002, 30 sun lalace, ko kuma an wofintar da su, wasu an saida su, saura guda biyu kacal.

Wannan ne ya sa Obasanjo ya kafa kwamitin da aka dora wa nauyin bin diddigin yadda aka kashe ko da taro da sisi ne a kamfanin, ta hanyar binciken takardu da rasidan biyan kudade da kuma kididdigar kudaden da ke shiga.

Kwamiti ya shafe shekara daya cur ya na aiki, inda a karshe ya fita da wani shirgegen kundin da ya tattara bayanan yadda aka cinye kudaden kamfanin. Kundin wanda saboda girman sa, an buga shi ne har juzi’i hudu.

An samu jami’an kamfanin, kamfanonin ejan na zirga-zirga, bankuna, kamfanonin cikin gida da na kasashen waje da hannu dumu-dumu cikin wannan harkalla.

Tun a ranar 11 Ga Disamba, 2002 da Majalisar Zartaswa ta umarci Sakataren Gwamnatin Tarayya a yi amfani da jami’an tsaro a karbo kudaden tare da hukunta masu laifi, har yau ba a kara tada maganar ba.

YADDA AKA RIKA SAIDA SASSAN JIRAGE GA ’YAN JARI-BOLA

Bincike ya tabbatar da cewa jami’an Nigeria Airways babu ruwan su da bin ka’ida, sun sace milyoyin daloli, sun rika bada kwangilar bogi, an rika narka makudan kudade a wasu bankunan da tuni sun durkushe.

Wani babban abin firgitarwa kuma shi ne yadda aka rika yi wa kantama-kantaman jirage farashin cinikin huhun goro, da kuma yadda aka rika balle kangarwar fika-fikai da sauran sassan jiragen ana saida wa ’yan rafta, wato jari bola.

Yayin da manyan jami’an kula da kamfanin suka rika jefa kudaden shiga da riba a cikin aljihun su, sun kuma rika karbar makudan kudade a bankuna a matsayin kamfani ne ya karbi bashi, amma sai su jidi kudaden su nausa cikin gidajen su.

GANI YA KORI JI: SUNAYEN WADANDA SUKA KARYA NJIGERIA AIRWAYS: Manyan cikin su na da kusanci da Buhari

1. Mohammed Joji

– Bayan da ya wawuri kudaden ya cika cikin sa, Mohammed Joji, wanda shi ne tsohon Babban Daraktan kamfanin, sai ya kafa Skypower Express Airways.

– Kwamitin bincike a lokacin ya bada shawarar cewa a haramta masa sake rike wani mukami a Najeriya, ko da kuwa manajan gidan wanka da bahaya ne.

– An kama Joji ya jidi naira biliyan 4.37 a cikin 1993 kacal, watau dala milyan 12 wadda kamfanin jirage na Swissair ya biya kudin ladar sauka da tashi ga Nigeria Airway, kuma Joji ya ragargaje kudaden.

– Ya karkatar da wata dala milyan 9.8, wadda ya ce wai ya biya Sabena Airline na Belgian. Bincike ya nuna cewa dala milyan daya kacal ya ba su.

– Akwai wata harkallar dala milyan 3.53, sai wata dala milyan 2.45, da kuma wata dala milyan 2.20 wadda ita ma aka ce ta yi fika-fiki ta tashi sama.

– A takaice a cikin watanni 24, Joji ya jidi dala milyan 30.018, watau sama da naira bilyan 11.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntube shi, ya ce laifukan da aka ce ya yi duk bi-ta-da-kulli ne Ministar Harkokin Sufurin Jirage ta Loakacin Obasanjo, Kema Chikwe ke yi masa.

Sai dai kuma abin takaici, gwamnatin Muhammadu Buhari ta nada shi shugabancin kwamitin fadada aikin titin filin jiragen sama na Abuja, kuma shi ne shugaban shirin maida jiragen Abuja sauka Kaduna a lokacin da ake aikin gyaran filin Abuja.

2. JANI IBRAHIM: JANI YA JA KAYA

A yanzu dai Jani su ne manyan ’yan jam’iyyar APC na jihar Kwara, ya yi shugabancin Nigeria Airways tsakanin 1996 zuwa 2001. Watau kenan su ne suka karasa binne gawar jiragen a rami, tunda a cikin 2002 ya durkushe.

A yanzu Jani darakta ne a Heritage Bank. Kwamitin bincike ya rubuta cewa: “Jani bai taba bada wata kwangila ba tare da ya yi harkalla a cikin ta ba.” An kara bayyana shi a matsayin “dan harkalla ne lamba daya.”

Rahoton kwamiti ya ce Jaji ya maida kudin kamfanin kamar gadon gidan su, kuma duk wanda ya ga zai iya kawo masa barazana, sai kawai ya kore shi daga kamfanin.

– Tsakanin 1997 zuwa 1999 ya cinye naira biliyan 1.47.

– Akwai kuma wata dala milyan 1.7 da kuma dala miliyan 1.2

– Gaba daya dai naira bilyan 3.63 ake nema a hannun sa, wadanda aka rasa yadda aka yi da su.
– Sai kuma wasu filaye 22 da ya raba wa wasu mutanen da ba ma’aikatan Nijeria Airways ba ne.

3. BERNARD BANFA Da PATRICK KOSHONI: ABOKIN DAMO GUZA

Dukkan su tsoffin manyan jami’an sojojin sama ne da suka yi ritaya. Banfa ya yi shugabancin kamfanin bayan ya yi ritaya daga aikin soja. Shi da Koshoni abokan cin mushe ne, ba mai boye wa kowa wuka kenan. tafiyar su daya, kuma tare suka yin harkalla.

– Su biyun sun hada baki, sun ciccibi girgi daya, kirar A310, suka saida a farashi mai rahusa, bayan an ba su shawarar kada su yi haka. Kwamiti ya ce su maido naira bilyan 158, watau dala miyan 435 na kudin wancan jirgi da suka sayar.

YADDA BUHARI YA NADA ’YAN HARKALLA CIKIN GWAMNATIN SA

– Babu wani tabbacin cewa su Banfa sun biya kudaden, amma dai abin da ya biyo baya shi ne, Banfa ya shiga tawagar guguwar Buhari ta CPC, wadda ta narke cikin APC a yanzu.

– Cikin 2016 Buhari ya yi wa Banfa sakayyar nada shi cikin Hukumar Gudanarwar Hukumar Kula da Yankin Neja Delta. Ita ce hukumar da aka fi narka wa makudan kudade a kasar nan.

4. AFAM NWAGBOSO: DARAKTAN ’YAN WASOSO

– Shi ne Daraktan Kula da Kudade, kuma duk kudaden da Nwagboso ya karba da sunan ajiye wa kamfani a bankin Continental Marchant Bank, babu su, babu dalilin batan su, kuma shi ma bankin ya mutu ya bar baya da kura.

5. OLU BAJOWA da ALABO GRAHAM-DOUGLAS

– Bajowa tsohon Manjo Janar ne, wanda bayan ya yi ritaya sai aka nada shi shugabancin Nigeria Airways tsakanin 1988 zuwa 1990.

– Ya bai wa wani ‘travel agency’ mai suna CES Travels ikon saida dukkan tikitin zirga-zirga daga Najeriya zuwa Amurka da kuma zuwa Ingila, har da zuwa da komowa duka.

– Cinikin da aka yin a miliyoyin daloli, kwatankwacin naira bilyan 2.6 a yanzu, duk an yi musu hadiyar kafino, domin ko sisi ba a saka aljihun gwamnati ba. Bajowa mai makogaron hadiyar daloli.

6. MOHAMMED KARI: KARI KU NE BUHARI
*An samu Kari da laifin cewa a 1993 lokacin ya na shugabancin Nicon Insurance ya hada baki da Nigeria Airways aka karkatar da dala milyan 13.9, kwatankwacin naira bilyan 50.82 a yanzu.
*Wannan Kari din dai ne Buhari ya nada shugaban kamfanin Insura na Kasa, NAICOM a cikin 2015, tun a farkon hawan sa shugabancin kasa.

PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Kari, dangane da inda aka kwana a kan zargin batan wadancan kudaden amma bai maida amsa ba. An yi masa tambayar ce ta hannun kakakin yada labaran hukumar, Rasaq Salami.

Sauran wadanda aka kira kananan berayen da suka jidi kudaden sun hada da:
7. Ibrahim Bala

8. All-Well Brown

9. Alexandra Howden

10. A. Olafisoye

Share.

game da Author