Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan marigayi tsohon ministan Ayyuka Tony Anenih.
Tony Anenih ya rasu yau a wani asibiti dake garin Abuja.
Buhari ya ce Najeriya ta yi rashin gwarzo kuma hazikin dan kasa.
Ya mika sakon ta’aziyyar da yin jaje ga iyalan mamacin.