Kamar yadda ta yi a baya, Gwamnatin Tarayya ta sake zuba ido ana ci gaba da wata sabuwar tankiya da tirka-tirka da Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiyar Ma’aikata (NHIS) na Kasa, Usman Yusuf.
Wannan sabuwar rigima da ta tirnike, ta afku ne a daidai lokacin da za a iya cewa wasan kwaikwayo ne a ka shirya, amma ba a taka rawar yadda aka so a taka ta din ba.
Cikin watan Juli, 2017, Majalisar Dattawa ta binciki Yusuf, Ministan Kiwon Lafiya ya dakatar da shi, Majalisar Tarayya ta jinjina masa, kwamitin binciken da minista ya nada ya kama shi da laifi, fadar shugaban kasa ta maida shi aiki daga dakatarwa, kuma an zarge shi da zuba kudin hukumar NHIS ta hanyar da ba ta dace ba.
Sannan kuma hukumar gudanarwar hukumar ta caccake shi bisa zargin cin hanci, karfa-karfa, cusa abin da babu a cikin kasafin kudi na hukumar da kuma karkatar da hankulan mambobin hukumar gudanarwar NHIS.
An sake rubuta masa takardar bincike, an dakatar da shi, inda daga bisani ma ya karya doka ya kutsa ofishin sa tare da rakiyar ’yan sanda. Yusuf ya bayyana cewa ba zai sake bin umarnin ministan lafiya ko wata hukumar gudanarwar NHIS ba.
Hakan ya sa babu wani takamaimen aikin da ake gudanarwa a hukumar kwanan nan, saboda ma’aikata da kungiyoyin kwadago na ma’aikatar lafiya sun raba kan su, kowane ya dauki bangare daya, su na barazanar barkewar rikici muddin a karshe aka mara wa wanda ba su so baya.
Cikin sauki mutum zai iya dora laifin a kan Yusuf da kuma masu daure masa gindi a fadar shugaban kasa, har ma a yi musu zargin nuna kabilanci da daure wa dan rigima gindi. Duk ma wata gaskiyar sa da ya ke tinkaho da ita, Yusuf dai ya yi wasu huldodin kudade masu matukar alamar tambaya. Ya kuma nuna shi babu wanda ya isa ya sa shi ko ya hana shi.
Don haka ba za mu dora laifin a kan sa ba, tilas mu dora laifin a kan sauran wadanda suka cancanta a dora a kan su.
Sau da yawa idan minista ya yi wani umarni, ba a bin umarnin na sa, sai ma a soke. An sha dakile kokarin sa na hukunta wanda ya yi ganganci ko kuskuren da ya cancanta a hukunta shi. Ko kuwa wadanda ba su goyon bayan sa su tayar masa da bore.
Duk wani kokarin da ya ke yi ba birge shugaban kasa ya ke yi ba. Sannan kuma akala da ragamar mulkin ma’aikatar da ke hannun sa, sai kara subuce masa take yi.
Hukumar Gudanarwar NHIS da ta kamata a ce ta gudanar da tsare-tsaren tafiyar da hukumar, rikice-rikice ya sa ba ta iya kaiwa ga nasara. Ta amince wa Yusuf ya zuba naira bilyan 30, amma daga baya ta dawo ta zarge shi da raina musu hankali.
Da a ce sun karanta Dokar da ta kafa Hukumar Inshorar Lafiyar Ma’aikata, da kuma sabuwar ka’idar Asubusun Bai-daya na TSA, da ba su tsoma kan su cikin wannan tsomomuwa ba.
Wannan hukumar gudanarwa da ta dakatar da Yusuf, wadda ita ma ana zargin ta da harkalla, ta ce Yusuf ya tafka kumbiya-kumbiyar kudade masu tarin yawa.
A takaice dai har yau babu wanda ya yi nasarar a jinjina masa a cikin wannan rikicin da ya ki ci, ya ki cinyewa, sai ma ita kan ta fadar shugaban kasa da ta zubar da girman ta, ta kasa shawo kan lamarin.
A daidai yanzu ake ta kokarin daura banten kokawar yakin neman zabe mai zuwa, bai kamata gwamnati ta yi sako-sako da wannan rikici ba, wanda zai iya janyo mata asarar kuri’u ta wata fuskar.
A karshe dai ‘yan Najeriya ne ke ji a jikin su dangane da jinkiri ko tsaikon da wannan rikici ya janyo, maimakon a taimaka musu su samu ingantacciyar kulawa a karkashin tsarin inshorar lafiya, amma rashin iya tafiyar da shugabanci ya lalata shirin.
Ya kamata Shugaban Kasa ya tashi tsaye ya magance wannan rudani. Ya daina nuna halin sa da ya saba na yin gum da bakin sa da kuma kau da kai da halin ko-in-kular da ya ke nunawa a wani muhimmin lamarin da ya shafi al’amurran kasar nan.
Discussion about this post