Hukumar EFCC ta kama Kwamandan Dakarun Zaman Lafiya, wato Nigerian Peace Corps, na Jihar Gombe, Ambore Enoch.
An kama Enoch ne a bisa zargin sa da ake yi da laifin badakala da kuma harkalla wajen daukar ma’aikatan jami’an tsaro na kungiyar dakarun.
An zargi Enoch da karbar zunzurutun kudade har naira milyan 54 da aka ce ya karba daga mutane daban daban masu neman aikin shiga cikin dakarun.
An ce ya karbi kudaden ne da nufin zai aimaka a dauke su kuma zai saya musu kayan shiga zuwa atisaye da tirenin damon ba su horo.
Kakakin EFCC na Jihar Gombe, Bello Bajoga, ya fitar da samarwa jiya Laraba cewa an damke Enoch ne bayan da suka samu takardun korafe-korafe daga wasu da abin ya shafa.
“Ana ci gaba da binciken yadda ya rika damfarar matasa musamman na nan jihar Gombe sun a biyan kudade daga naira 3,000 har zuwa 60,000. Kudaden su na nan damfare a cikin wani asusu na wani banki. Yanzu haka abin da ya karba sun kai naira miliyan 54.”Inji Bajoga.
Ya ce an karbi kudaden tsakanin Disamba 206 zuwa Maris, 2017.
Ya kara da cewa amma EFCC ta gano cewa Enoch ya cire naira miliyan 3.5 ya yi amfani da ita, ya tura naira milyan 20 a cikin asusun sa, sannan ya bai wa hedikwatar ‘Peace Corps’ da ke Abuja naira miliyan 18.