YAJIN AIKI: Duk wanda ya ki zuwa aiki zai rasa albashin sa – Gwamnatin Tarayya

0

A taron ta jiya Labara a Fadar Shugaban Kasa, Majalisar Zartaswa ta amince da yin amfani da tsarin hana albashi ga duk ma’aikacin gwamnatin tarayya da ya kuskura ya tafi yajin aiki.

Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ne ya bayyana haka ga manema Labarai, bayan fitowa daga taron da suka yi, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Ngige ya nuna damuwar cewa aikin gwamnati a kasar nan a cukuikuye ya ke da dimbin matsaloli da rikita-rikita a wasu fannoni da yawa, shi ya sa gwamnati inji shi ta rika kafa kwamitoci da nufin magance wadannan matsaloli da kuma shawo kan hardaddun lamurran da suka dabaibaye aikin gwamnati.

Ya ce kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa tun cikin watan Agusta, 2016, ya damka rahoton sa cikin Oktoba, 2017, wanda kuma shi minista Ngige na cikin wadanda suka duba matsalolin.

Ngige ya ce akwai batu kan tankiyar da ke cikin dokar aikin kwadago ta 2004, sashe na 43. Dokar ta ce idan ma’aikata ko masana’anta ta kulle kofar shiga ta hana ma’aikaci shiga cikin ninda ya ke aiki, to za ta biya shi ladar sa ko albashin sa na tsawon awa ko kwanakin da ya yi bai shiga wurin aiki ba.

“Amma idan ya tafi yajin aiki, to za a cire masa kudaden adadin kwanakin da ya yi bai je aiki ba, ya tafi ya na yajin aiki. Wannan batu na cire albashi kuwa shi ma duk ya nan kunshe a cikin sashen da doka ta ce idan ka hana ma’aikaci shiga ofis to za ka ci gaba da biyan sa.”

Har ila yau Ngige ya kara da cewa babu samun kudin fansho ga duk wani ma’aikacin da ya tafi yajin aiki na iyar kwanakin da ya yi bai je wurin aiki ba.

Ministan ya ce Majalisar Zartaswa ta amince da yin amfani da wannan tsari ne a zaman ta wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya Laraba a Fadar sa.

Bayan wannan kuma, ya ce a zaman na su, sun duba yadda wasu shugabannin kungiyoyin kwadago ke kasancewa cikin shugabancin kunyiya har tsawon rayuwar su, ko kuma tsawon shekaru da suke aiki har sai sun yi ritaya.

Ya ce haka kawai wasu za su rika kafa makauniyar hujjar cewa su na shugabancin kungiya, don haka ba su so a yi musu canjin wurin aiki daga wani gari zuwa wani ko daga wata ma’aikata zuwa wata. Ko daga wani sashe ko wuri zuwa wani.

“Duk tsiyar ka dai ai sai ka zama ma’aikacin gwamnati kafin ka zama mamba na shugabannin kungiyar kwadago. Don haka tilas din ka ne ka rika bin dokokin aikin gwamnati.” Inji Ngige.

Ya ce a cikin wannan rahoton kwamiti, gwamnati ta ce za ta duba wannan matsaloli, kuma dole an rika gindaya dokoki da sharuddan iyakar wa’adin da dan kungiyar kwadago zai yi a cikin kungiya, ba wai haka kawai ka na aikin gwamnati ba kuma ka yi wa kungiyar kwadago shiga-sojan-Badakkare.

Daga nan ya ce daga yanzu tilas dukkan kungiyoyin kwadago sai sun rika gabatar da ka’idoji da wa’adin da shugabannin kungiya za su yi su kammala wa’adin shugabancin su.

A kan batun albashi mafi karanci, kuwa, Minista Ngige ya ce Gwamnatin Tarayya ta tsaya kan bakan ta cewa daga naira 24,000 ba za ta kara ko sisi ba.

Share.

game da Author