Gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 1.5 wa talakawa 20,344 a jihar Bauchi

0

A ranar Litini ne jami’in shirin tallafa wa talakawa ( CCT) Jibrin Yusuf ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta raba Naira biliyan 1.5 wa talakawa 20,344 a jihar Bauchi.

Yusuf ya fadi haka ne a lokacin da wakilan kungiyar manema labarai mata na kasa (NAWOJ) suka kawo masa ziyara a ofishin sa dake garin Bauchi.

Ya ce shirin CCT ta fara raba wadannan kudade ne tun a farkon shekarar nan zuwa wannan lokaci. Sannan yace shirin za ta saka wasu talakawa 2,969 domin su samun wannan tallafi.

” Mun kuma horas da wadannan mutane wanda kashi 80 bisa 100 cikin su mata ne kan sana’o’in hannu da hanyoyin shiga cikin kungiyoyin adashi domin taimakawaa kawunan su.

A kashe shugaban kungiyar NAWOJ Bulak Afsa ta bayyana cewa sun zo ne domin jinjina wa shirin CCT bisa wannan kokari da suke yi wa talakawa a wannan jiha.

” Gudunmawar da za mu bada muku ma a matsayin tukuici shine na wayar da kan kungiyoyin yin da suke da rajista kan hanyoyin da zasu bi wajen samun basuka a bankunan dake jihar.”

Share.

game da Author