An yi wa yara miliyan 1.5 allurar rigakafin cutar shan inna a jihar Jigawa

0

Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Jigawa (JSPHCDA) Kabiru Ibrahim ya bayyana cewa zuwa yanzu hukumar ta yi wa yara miliyan 1.5 allurar rigakafi cutar shan-inna a jihar.

Ibrahim ya fadi haka ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Litini a garin Dutse.

Ya ce sun samu nasarar yin allurar rigakafi a kananan hukumomi 27 na jihar a dalilin samun isassun magunguna da gwamnati ta tanada.

A karshe Ibrahim ya jinjinawa sarakunan gargajiya, malaman addini, masu fada a ji da iyaye da su rika goyan bayan da suke samu a duk lokacin da suke gudanar da allurar.

” Samun goyan bayan irin haka zai taimaka wajen hana bullowa kawar da cututtuka a jihar da kasar gaba daya.”

Share.

game da Author