Bincike ya nuna cewa mutanen dake fama da cutar ‘Sarcoma’ basu samun kular da ya kamata su samu a kasashen duniya.
‘Sarcoma’ cuta ce dake kama gabobi, kasusuwa, nama da kitsen mutum wanda idan ba a gaggauta garzayawa asibiti ba akan fada cikin gagarumin matsala.
Wani likita mai suna Peter Hohenberger daga asibitin jami’ar Mannheim a kasar Jamus ya gano haka a wani bincike da ya gudanar.
Ya ce har yanzu dai babu tabbacin yadda ake kamuwa da wannan cutar amma akwai yiwuwar cewa amfani da sinadarorin dake cutar da kiwon lafiyar mutum na kawo wannan cutar.
Bayan haka wani likita a jami’ar ‘Paris Descartes’ a kasar Faransa mai suna Audrey Bellesoeur ya tabbatar da haka.
Discussion about this post