Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajinta wa iyayen marigayiya Hauwa Liman da Boko Haram suka hallaka.
Idan ba a manta ba Boko Haram sun dauke Hauwa Liman ne tare da wasu ma’aikatan agaji na Red Cross a sansanin Rann in da suke aikin samar da kiwon lafiya ga mazauna wannan sansani.
A wayar tarho da Buhari yayi kai tsaye da Mahaifin marigayiya Hauwa, Mohammed Liman, ya jajinta masa sannan ya bayyana masa cewa gwamnati tayi kokarin ceto Hauwa amma Allah bai yi ba.
Bayan haka ya jajinta wa shugaban kungiyar Red Cross, Peter Maurer bisa wannan rashi da kungiyar ta yi.
Ya roki kungiyar da kada ta dakatar da aikin da take yi a Najeriya bisa wadannan abubuwa da suka faru.
A watan da ya gabata, Boko Haram sun kashe Saifura Khorsa, wanda ita ma ma’iakaciyar Red Cross din ne.
Kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ne ya fitar da wannan sako.