Gwamnan Adamawa ya jaddada mubayi’ar sa ga Buhari da APC

0

Gwamna Bindow Jibrilla na jihar Adamawa ya bayyana cewa har yanzu biyayyar sa na nan daram ga Shugaba Muhammdu Buhari.

Ya yi wannan jawabi ne a daidai lokacin da ya ke nuna damuwa kan zargin da ya ce wasu ‘yan siyasa da bai ambaci sunayen su ba ke kokarin shafa masa bakin fentin kawo sabani tsakanin sa da Shugaba Muhammdu Buhari.

Da ya ke magana ta bakin Kwamishinan Yada Labarai na Jiha, Ahmed Sajoh, gwamna Bindow ya ce wasu ‘wasu algunguman ‘yan siyasa’ na nan na tsara yadda za su buga fastar gwamnan tare da ta Atiku Abubakar, wanda ya ci zaben fidda-gwanin jam’iyyar PDP na takarar shugaban kasa kwanan nan.

Atiku Abubakar shi ne ubangidan Gwamna Bindow.

Sajoh ya ce algunguman sun yi niyyar lika fastocin a Yola da kuma Abuja.

Bindow ya kayar da Mahmood Ahmed, wanda dan uwa ne ga Aisha Buhari da kuma daya daya dan takarar, Nuhu Ribadu a zaben fidda-gwani.

Ba a dai sani ba ko Bindow na nufin daya daga cikin su ne, amma di su biyun duk sun yi Allah wadai da sakamakon zaben da aka ce gwamnan Bindow din ne ya yi nasara, kuma sun nemi a soke zaben.

“Bari na kara jaddada muku cewa Gwamna Bindow ba shi da niyyar barin jam’iyyar APC, kuma ba zai yi wa kowa aiki a asirce ba. Sannan kuma ba zai goyi bayan kowane dan takara da ba dan APC ba.

Sajoh ya kara da cewa idan aka yi la’akari da ayyukan da gwamnatin tarayya ta yi a jihar Adamawa, to babu dalilin da wani dan jihar ba zai goyi bayan APC ba.

Sai dai kuma wakilin mu ya lura da cewa tuni fasta mai dauke da hoton Bindow da na Atiku ta fara karade Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Share.

game da Author