Ba ni da shafin sada zumunta a soshiyal midiya -IBB

0

Tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Babangida ya nesanta kan sa daga duk wasu shafukan sada zumunta a soshiyal midiya wadanda ake danganta sunan sa da su.

Cikin wata watakarda da ofishin yada labaran sa ya fitar jiya Lahadi da dare, a shafin ofishin na Twitter, sanarwar ta ce duk wani shafi da aka gani dauke da sunan sa ko hoton sa to ba na sa ba ne.

Wannan ya biyo bayan wata sanarwa ce da wani shafi da aka danganta da shi ya buga, inda Babangida din ya taya Atiku Abubakar murnar lashe zaben fidda-gwani na jam’iyyar PDP a matakin zaben shugaban kasa.

Don haka sanarwar ta kara da cewa Babangida ba shi da hannu da masaniya a dukkan wadannan kafofi ko wata kafa da aka alakanta da sunan sa ko hoton sa.

Share.

game da Author