PCN ta rufe shagunan siyar da magani 165 a jihar Delta

0

Shugaban kungiyar masana magunguna ta Najeriya rashen jihar Delta Anthonia Aruya ta bayyana cewa kungiyar ta rufe shagunan siyar da magani 165 a jihar.

Aruya ta bayyana haka ne da take ganawa da manema labarai a Asaba inda ta kara da cewa bayan rufe wadannan shaguna sun tasa keyar wasu mutane bakwai da ake zargin suna da hannu a safarar magungunan da basu da aminci.

Ta ce sun rufe wadannan shaguna ne saboda karya dokokin kungiyar wanda suka hada da rashin rajista,rashin tsaftace wuraren ajiyan magungunan su, siyar da magungunan da gwamnati ta hana, siyar da magunguna ba tare da izinin likita ba ko kuma ma’aikacin kiwon lafiya da sauran su.

Aruya ta kuma kara da cewa kungiyar ta gano haka ne a dalilin binciken shagunar siyar da maganin da kungiyar kan gudanar lokaci lokaci.

Ta ce kungiyar za ta wayar da kan masu ruwa da tsakin dake fannin siyar da maguguna kan kiyayae dokokin kungiyar domin kare kiwon lafiyar mutane.

A karshe Aruya ta yi kira ga mutane da su guji siyan magani a shagunan da basu da rajista, magungunan da basu dauke da kwanakin daina aiki da dai sauran su.

Share.

game da Author