A Ranar litinin gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya bayyana a jihar cewa baya goyon bayan shawarar yakice shugabannin jam’iyya da uwar jam’iyya ta yi a zaben fidda gwani da za a yi a jihar.
Za a yi zaben ne ta tsarin kai tsaye, wato ‘Kato bayan Kato’
Idan ba a manta ba sau biyu dai ana dage zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar Zamfara.
‘Yan takara kusan 10 ne ke kokawar zama dan takarar gwamna a jihar a jam’iyyar APC.
Duk da haka shugaban shirya zaben fidda gwanin na jam’iyyar Abubakar Fari ya ce ba za su saurari gwamnan ko su biye masa ba.
” Mu fa a shirye muke, mufa ba za mu dakatar da shirye-shirye ba. Muna kan bakar mu na gudanar da zaben fidda gwanin kamar yadda aka tsara a jihar, ba ta gwamna muke ba.
Taron da ake yi yau taro na yadda za a shirya matakan tsaro a jihar a lokacin zaben.