Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya bayyana cewa yana nan a cikin jerin ‘yan takarar fidda gwani na gwamnan jihar Adamawa da za a yi ranar Alhamis a garin Yola.
Salihu Banwo, shugaban kwamitin kamfen din Ribadu ne ya sanar da haka a hira da yayi da manema labarai a garin Yola.
” Dama can babban dalilin da ya sa Ribadu ya janye daga takarar fidda gwani shine ganin yadda wasu suka yi babakere a zaben sannan da kamar ba za a yi adalci a zaben ba.
” Amma tunda yanzu haka uwar jam’iyyar daga Abuja ta gyara tsarin zaben hankalin mu ya kwanta kuma mun tabbata za ayi adalci a zaben. Muna kuma sa ran mu ne za mu yi nasara.
Ribadu ya ce yana nan daram a takarar.
Jam’iyyar APC ta tsayar da ranar Alhamis, ranar zaben fidda dan takarar gwamnan jihar Adamawa sannan ta canja shirin zabe daga na wakilai zuwa kato bayan Kato.