Ministan Harkokin Waje Geoffrey Onyeama, ya soki lamirin kasa Switzerland cewa ta na da hannu a harkallar kimshe makudan kudade da tsohon shugaba na mulkin soja, Sani Abacha ya yi a kasar a lokacin ya na kan mulki.
Onyeama ya yi zargin cewa saboda kasar na da hannu da kuma masaniya ne shi ya sa ta ke kakaba tsauraran sharudda da matakan dawo da ilahirin kudaden gida Najeriya.
Wadannan kudade dai su ne makudan kudaden da Abacha ya rika sacewa ya na kimshewa a kasashen waje, wadanda akasarin su duk miliyoyin daloli ne.
Kwanan nan ne kasar Switzerland ta amince za ta maido wa Najeriya dala 350 daga cikin makudan kudaden da Abacha ya kimshe a kasar.
Ministan ya ce hankalin sa ya yi matukar tashi kuma ya fusata matuka ganin irin kudaden da Switzerland ta rike wadanda a yanzu ke a hannun wasu cibiyoyi da wasu lauyoyi a kasar.
Onyeama ya yi wannan furuci ne a yau Talata yayin da ya ke jawabi a wurin taron shekara-shekara karo na biyu a Cibiyar Taro ta Kasa-da-kasa a Abuja.
An shirya taron ne domin tattauna hanyoyin da za a bi a hana sace kudade ana kimshewa kasashen waje, tare kuma da gano hanyoyi masu sauki da za a rika bi domin a dawo da wadanda aka rigaya aka sace aka boye a waje.
Onyeama ya fassara matakan da kasar Switzerland ta dauka a matsayin fashi da makami ne karara da rana tsaka.
Daga nan sai ya ce kasar Switzerland na da masaniyar irin kudaden da ake sata ana kimshewa a kasar.
Sai ya ce ai dama an ce abokin barawo, shi ma barawo ne.’ Ko kuma a ce mai adana wa barawo kayan sata ai shi ma barawo ne.
Ya ce kashi 60 zuwa 65 bisa 100 na kudaden Afrika da ake sacewa, duk ana fitar da su ne ta hanyar hadin baki da manyan kamfanoni na duniya.
Discussion about this post