Kungiyar ‘Amnesty’ ta nemi Najeriya ta buga sakamakon zargin cin zarafin jama’a da sojoji ke yi

0

Kungiyar jin kai ta duniya, da aka fi sani da ‘Amnesty International’, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta fitar da rahoton da kwamitin da shugaban kasa ya kafa a kan binciken zargin take hakkin jama’a da sojoji ke yi.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya kafa kwamitin a cikin Agusta, 2007, a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ke hutun jiyya a Landan sakamakon wata rashin lafiyar da har yau ba a bayyana ko wace iri ba ce.

Kwamitin wanda ke karkashin shugabancin Mai Shari’a Biobele Georgewill na Kotun Daukaka Kara, ya kammala binciken sa kuma ya mika tun cikin watan Fabrairu, 2018, amma har yau gwamnati ba ta yi komai a kai ba.

Wannan shiru da kuma kau da kai daga daukar mataki da gwamnatin tarayya ta yi, abin damuwa da takaici ne kwarai ba kadan ga, inji ‘Amnesty International’.

A lokacin da aka kafa kwamitin, sojojin Najeriya na matukar fuskantar zargin cin zarafin jama’a ciki har da kisan gillar sama da mabiya Shi’a 300 a Zaria cikin 2015, kashe wasu gungun ‘yan kungiyar Biafra a Kudu maso Gabas da kuma irin gallazawar da ake wa wasu da ake zargi da Boko Haram a Arfewa maso Gabas.

Sai dai kuma Humumar Tsaro ta Sojoji sun rika hakikicewa cewa jami’an su na gudanar da ayyukan da dokar kasa ta gindaya musu a kan ka’ida da nuna kwarewa, ba tare da wuce-gona-da-iri ba.

Tsakanin 11 Ga watan Satumba da kuma 8 Ga Nuwamba, 2017, kwamitin binciken ya zauna a garuruwan Abuja, Maiduguri, Fatakawl, Enugu, Kaduna da Lagos a cikin kwanaki 90 na wa’adin da aka ba shi.

Sun binciki zargin kashe jama’a ba tare da yanke musu hukunci ba, azabtarwa, fyade, bacewar mutane ko sama ko kasa da kuma banka wa kauyuka wuta da aka zargi sojoji sun rika yi.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Wale Fapohunda, Hauwa Ibrahim, Ifeoma Nwakama da kuma wakili daga ofishin Mai Bada Shawara na Musamman a Harkokin Tsaro.

Cikin watan Oktoba, 2017 ne Amnesty International ta zauna tare da kwamitin inda ta damka masa binckiken da kungiyar ta fitar dangane sojojin.

Share.

game da Author