Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa ba zai taba janye wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar takarar shugabancin kasa na 2019, da ya ke yi a karkashin jam’iyyar PDP ba.
A jiya ne bayan wani taro da Atiku ya yi da jiga-jigan PDP na jihar Jigawa, ya ce ya yi amanna cewa Lamido zai iya janye masa takara, a matsayin sa na yayan sa.
Atiku ya ce kasancewa Lamido kani ne a gare shi, ya yi amanna da cewa zai iya janye masa, tunda dukkan su biyu din akidar siyasar su daya.
Atiku ya shaida wa mahalarta taro Dutse, babban birnin jihar Jigawa cewa mahaifiyar sa ‘yar asalin kauyen Jigawar Sarki ce, da ke cikin karamar hukumar Dutse, kafin iyayen ta su yi hijira zuwa jihar Adamawa, inda a can ne ta haifi Atiku.
Da ya ke maida wa Atiku martani, ta cikin wata sanarwa da kakakin yada labaran Lamido din ya saka wa hannu, Adamu Usman ya ce Lamido ba zai taba janye wa Atiku ba.
“Eh, tabbas Atiku ya girmi Sule Lamido, amma idan ana maganar siyasa, ai ni yayan sa ne, shi yaro ne. Saboda a lokacin da ina Majalisar Tarayya cikin 1979, Atiku bai yi ritaya daga aikin kwastam ba ma.
“Idan kuma Atiku ya ce za a bi ta yawan shekaru ne a zabi dan takara, to shi ya janye ya kyale wa Buhari mana, tunda dai shi ma ai Buhari ya fi shi yawan shekaru.”
Usman ya ci gaba da cewa, “Lamido ya nuna juriya, hakuri, biyayya, da kuma tsayawa ka-in-da-na’in a kan raya jam’iyya da inganta tafarkin dimokradiyya, duk kuwa irin bibiyar da ake nuna masa.
“Kai ko ma da a ce Lamido bai nuna sha’awar zai tsaya takarar zaben shugaban kasa ba, to PDP sai ta kira shi ta ba shi tuta. Kuma idan ana maganar a janye ne a bar wa wani dan takara, to Lamido ne ya kamata a janye a bar masa takarar, saboda ya fi dukkan sauran karsashi da kyakkyawar alkiblar ayyuka, kwarewa, sanin makamar siyasa da kuma karfin iya kokawa da jam’iyyar APC.”
“Shin idan har ma Lamido ya san zai iya janye wa wani, to don me zai fito takarar ma tun da farkon fari?” Haka Usman ya nanata.
Lamido, wanda da shi aka kafa jam’iyyar PDP, tun da aka kafa jam’iyyar har yau bai taba ficewa daga cikin ta ba.
Discussion about this post