Likitocin Asibitin LASUTH sun fara yajin aiki

0

Kungiyar likitoci (ARD) dake aiki a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Lagas ta shiga yajin aikin kwana uku.

Likitocin sun fara wannan yajin aiki ne ranar 2 ga watan Satumba inda suke kira ga gwamnati da ta karo ma’aikata da likitoci a asibitin.

Shugabancin kungiyar na rikon kwarya Ibrahim Ogunbukola ya bayyana cewa fara wannan yajin aikin ya zama dole saboda rashin likitoci da asibitin ke fama da shi da hakan rage ingancin aiyukkan da suke yi a asibitin.

” Duk da cewa mun fara yajin aiki za mu ci gaba da duba marasa lafiya dake bukatar kula na gaggawa.

Ogunbukola ya jaddda cewa da zaran kwanki ukun da suka ba gwamnati sun cika, za su dakatar da aiki kwata-kwata har sai an biya musu bukatun su.

A karshe kwamishinan lafiya na jihar Jide Idris ya roki likitocin da su janye wannan yajin aiki da suka fara cewa yana gab da samun izinin gwamnati kan karo ma’aikata a asibitin kamar yadda suka bukata.

Ya ce gwamnati na sane da matsalolin su sannan tana iya kokarin ta don ganin ta biya bukatun nasu.

Share.

game da Author