Mata ta kashe kanta a dalilin kama mijinta da wata a gadon su na aure

0

Wata matar aure mai suna Kafilat ta kwankwadi ruwan guba a dalilin kama mijinta Ismail da ta yi da wata a kan gadon su na aure.

Wannan mummunar abu ya faru ne ranar Laraba gidan su dake unguwar Egan-Igando, jihar Legas.

Dama can Kafilat Oriade ta yi yaji daga gidan mijinta mai suna Ismaila Oriade kan matsalar yawan neman mata da mijin ke yi.

Wani makwabcin su ya bayyana wa PREMIUM TIMS cewa wannan ba shine karo na farko ba da Kafilat take kwankwadan ruwan guba iadan suka sami sabani da mijinta.

” Ko a kwanankin baya sai da Kafayat ta kwankwadi ruwan guba, Allah ne ya sa ran ta na gaba.

” A wannan karo abin ya zo da ajali. Domin kuwa bayan ta sha wannan ruwan guba muka gaggauta kaita asibiti har guda biyu. Da suka ga halin da take ciki sai suka ki amsar ta, ana haka ne ta Allah yayi mata cikawa.

Mijin nata, wato Ismail ya bayyana cewa shi dama tuni sun rabu da Kafilat duk da cewa ba a san inda yake ba a lokacin domin ya gudu.

Share.

game da Author