Bismillahir Rahmanir Rahim
Ya ku Bayin Allah! Lallai dukkanin mu muna kwadayin samun rahamar Allah, jinkan sa da tausayin sa. Kuma babu mai yanke kauna daga rahamar Allah sai mutanen da suke halakakku, tababbu. Domin samun rahamar Allah, jinkan sa da tausayin sa, dole ya zamanto muna kiyaye ayukka kamar haka:

1. Nuna Rahama, Jinkai da tausayi ga bayin Allah da halittunsa
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Kuyi rahama da jinkai ga wadanda suke kasa da ku (wato bayin Allah), sai wanda yake sama da ku (wato Allah) ya jikan ku.” [Abu Dawuda ne ya ruwaito shi]
Kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Sani dai kadai Allah yana jinkan bayin sa ne masu jinkai.” [Sahihul Jami’ na Shaykh Albani]
Kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Koda akuya ce kayi jinkai a gare ta, to kai ma Allah zai jikan ka.” [Silsila as-Sahiha na Shaykh Albani]
2. Yin ihsani, wato kyautatwa zuwa ga Allah da kuma bayin Allah
Allah Ta’ala yana cewa:
“Lallai rahamar Allah da jinkan sa suna kusa ga dukkan masu kyautatawa.”
3. Yin Da’a da biyayya ga Manzon Allah (SAW)
Hakika rahamar Allah tana sauka ga masu biyayya ga Manzon sa. Allah Madaukaki yana cewa:
“…Kuma kuyi Da’a da biyayya ga Manzon Allah saboda ku samu rahama da jinkai.”
4. Yin rangwame da nuna tausayi a cikin kasuwanci
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Allah zai yi rahama da jinkai ga mutumin da yake ramgwame idan zai sayar da abin sayarwa, kuma zai yi rangwame idan zai saya, kuma zai kyautata idan zai biya bashi.” [Bukhari ne ya ruwaito shi]
5. Zuwa duba marar lafiya
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Dukkan wanda yaje duba marar lafiya yana tafiya ne a cikin rahamar Allah.” [As-Silsilah as-Sahihah na Shaykh Albani]
6. Wanda ya tashi yin Nafilar dare kuma ya tayar da iyalinsa zai samu rahamar Allah
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Allah yayi rahama da jinkai ga mutumin da ya tashi yin sallar nafilar dare, kuma ya tada matarsa ita ma tayi, idan bata tashi ba sai ya shafa mata ruwa a fuska domin ta tashi.” [Abu Dawuda ne ya ruwaito shi]
7. Yin aski a lokacin aikin Hajji da Umarah
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Ya Allah kayi rahama da jinkai ga masu yin aski a lokacin aikin hajji, ya fadi haka har sau uku.” [Sahihul Bukhari]
8. Zama a wurin da ake ambaton Allah ko wurin karatu ko daukar darasi ko wurin wa’azi
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Babu wasu mutane da zasu zauna suna ambaton Allah a natse, face Mala’iku sun zagaye su, kuma rahamar Allah da jinkan sa ya lullube su…” [Muslim ne ya ruwaito shi]
9. Zama a Masallaci bayan an gama Sallah da nufin jiran wata Sallar ko don ambaton Allah ko daukar darasi
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Lallai Mala’iku suna nema wa wasu gafarar Allah matukar suna zaune a wurin da suka yi Sallah, suna cewa: Ya Allah kayi masu gafara, Ya Allah kayi masu rahama.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]
10. Karanta Hadisin Manzon Allah, da aiki da shi, da isar da sakonsa zuwa ga mutane
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Allah yayi rahama da jinkai, a wata ruwayar, Allah yayi dubin rahama da jinkai ga dukkan mutumin da yaji wani abu daga gare ni, sannan ya isar da shi kamar yadda yaji shi, sau da dama wanda yaji Hadisin yana iya fin wanda ya fada masa fahintar sa.” [Sahihul Jami’ na Shaykh Albani]
11. Yin shiru lokacin karatun Alkur’ani da lokacin sauraron sa
Allah Madaukaki yana cewa:
“Idan ana karanta Alkur’ani to kuyi shiru ku saurara, tabbas yin haka zai sa ku sami rahamar Allah da jinkan sa.”
12. Yawaita fadar Alhamdulillahi Kathiran
Manzon Allah (SAW) yana cewa:
“Idan bawa yace; Alhamdulillahi Kathiran, sai Allah yace, ku rubutawa bawa na rahamata mai yawa.” [Silsilatul as-Sahihah na Shaykh Albani]
Ya Allah kayi wa Mahaifan mu rahama da jinkai, ka gafarta masu dukkanin laifukan su, ka daukaka darajar su, ka sanya su a Aljannah, ka haskaka kabarin su, ka kare su daga azabar kabari da azabar wuta, su da dukkanin sauran Musulmai baki daya da suka riga mu gidan gaskiya. Allah ka sa mu cika da kyau da imani, Amin thummah amin.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jahar Kogi, Nigeria. Za ku same shi a gusaumurtada@gmail.com ko +2348038289761.
Discussion about this post