Likita yace ba kowace irin yanayi na damuwa bane ke cutar da lafiyar mutum

0

Wani likita a babbar birnin tarayya Abuja Gregory Mowete ya bayyana cewa ba kowani irin damuwa bane ke cutar da kiwon lafiyar mutum.

Mowete fadin haka ne yayin da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ke hira da shi a Abuja ranar Laraba.

Likitan ya bayyana cewa damuwa wani irin yanayi na takura ne da jikin mutum kan shiga ta hanyar yawan tunani, aiki ba hutawa da kuma sauran su.

Ya kuma ce a lokacin da mutum ke cikin tsanannin damuwa jikin sa kan amayo wasu sinadarori biyu ‘Adrenaline’ da ‘Cortisol’ da ke kare lafiyar mutum.

‘‘Misali idan mutum ya firgita ko ya ji tsoro farad daya, Sindarin Adrenaline na taimaka wa mutum wajen kare sannan sinadarin Cortisol ne ke hana mutum kamuwa da bugawar zuciya, suma ko kuma hawan jini.

Bayan haka likitan ya jawo hankalin mutane game da alamomin damuwar da ke cutar da kiwon lafiyar mutum wanda suka hada da rashin cin abinci, rashin hulda da mutane, kunci da sauran su.

A karshe Mowete ya ce shiga cikin mutane, motsa jiki, cin abincin dake kara karfin garkuwan jiki na cikin hanyoyin gujewa irin wadannan matsala.

Share.

game da Author