Bada tazarr iyali dabara ce da kungiyoyin kiwon lafiya suka shigo da shi domin inganta kiwon lafiyar mata da yara.
Sai dai kuma wannan shiri wasu al’adun da addinai ba su amince da shi ba.
Misali bincike ya nuna cewa a Najeriya wasu al’adu da addinai na kyamar mace mai aure ta yi amfani da dabaran bada tazaran iyali sannan idan mace mara aure ta yi amfani da shi sai ayi mata gani fasika ce.
Amma likitoci sun bayyana cewa amfani da dabarun bada tazarar iyali hanya ce dake hana mata zubar da ciki da fadawa cikin hadarin da ke aukuwa da haka.
A dalilin haka ne kungiyoyin kiwon lafiya tare da hadin guiwar gwamnatin tarayya suka kebe ranar 26 ga watan Satumba na duk shekara domin wayar wa mutane kai game da amfanin da dabarun bada tazarar iyali.
Kungiyoyin kiwon lafiya sun kuma bayyana wasu dabarun bada tazarar iyali shida wanda mata za su iya amfani da shi cikin sauki.
Ga Dabarun
1. ALLURA: Wannan dabarar bada tazaran iyalin iri biyu ne, akwai wanda ke kare mace daga daukar ciki na tsawon wata daya da kuma wanda ke kare mace na tsawon watanni biyu.
2. KWAYAR MAGANI: Wannan dabara ce da mace zata rika hadiyar kwayar magani kullum. Likitocin sun bayyana cewa kwayoyin na da inganci idan mace na amfani da su yadda ya kamata.
3. ASHANAR HANNU: Wannan dabarar na da ingancin kare mace daga daukar ciki na tsawon shekaru uku zuwa biyar. Ma’aikatan kiwon lafiya kan saka wa mace a habar hannun ta sannan likitocin sun bayyana cewa dabaran kan kara yawan zuban jini na wata wata da suke yi.
4. DABARAR DA AKE SAKA WA A MAHAIFA: Wannan dabarar na kare mace daga daukar ciki na tsawon shekaru biyar zuwa 10 sannan bisa ga bayanan likitoci shima yana kara wa mace yawan zuban jini na wata- wata.
5. SHAYARWA: Likitoci sun bayyana cewa ba kowace mace ne take iya yin wannan dabara ba. Dabarar na aiki ne idan mace mai shayarwa bata ganin al’adan ta na wata-wata.
6. KORORO ROBA: Roba ne da mata ko maza kan saka kafin su sadu. Kororo roba na kare mata daga daukar ciki sannan da samar da kariya daga kamuwa da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar saduwa kamar su kanjamau, Hepatittis, ciwon sanyi da sauran su.