Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa Faransa za ta kara yawan gudunmawar da kasashen dake ci gaba musamman kasashen nahiyar Afrika ke samu daga gareta domin ilimantar da mata.
Macron ya fadi haka ne a taron ‘Goalkeepers’ da aka yi a kasar Amurka ranar Laraba.
Ya ce suna sa ran daga 2020 zuwa 2030 kasar ta kara yawan wannan gudunmawar daga dala miliyan 10 zuwa dala miliyan 15.
Macron ya kara da cewa burin sa shine ya ga ya taka muhimmiyar rawa wajen kawar da illolin dake tattare da canjin yanayi, ilimantar da mata da kawar da fifita jinsin maza fiye da na mata.
” A dalilin haka ne muka amince mu kasa wannan tallafi da za mu bada domin shawo kan wadannan matsalolin dake neman yi wa kasashen katutu.
Ya ce ilimantar da mata hanya ce da zai taimaka wajen kubutar da kasahsen Afrika daga kangin kara yawa musamman yadda kasashen ke fama da karancin ababen more rayuwa.
Discussion about this post