Kungiyar Ma’aikata na fadin kasar nan sun yanke shawarar cewa za su fara yajin aikin fushin rashin cika musu alkawarin karin albashi da Gwamnatin Tarayya ta ki yi.
Sun yanke wannan shawara ce a yau Talata.
A cikin wata takardar bayann tashi taro Sakatare Janar na kungiyar, Musa-Lawal Ozigi ya sa wa hannu, bayan da Kwamitin Zartaswar kungiyar ya zartas da amincewa a fara yajin aikin.
“Mu na sanar da fara yajin aiki daga ranar Alhamis, 27 Ga Satumba, 2018” Inji Ozigi.
Daga nan ya kara da cewa sakamakon haka za su tashi tsaye domin nusasshe da ‘yan kungiyar a duk inda suke su fara shirin yajin aiki daga Alhamis da sassafe.
Ya ce ya na bada shawara ga dukkan ma’aikata kungiyoyi da sauran talakawa cewa su tanadi kayan abinci tuli guda kowa ya kimshe a gida.
Ya ce ba kayan abinci kadai ba, har dukkan kayan amfani da tasarifi na cikin gida na yau da kullum, duk kowa ya tanada a adaba,
Daga nan sai ya yi kira ga kungiyar ma’aikatan da ta hada kai da kungiyar kwadago ta jihohi domin yajin aikin ya yi tasiri sosai a jihohi
An dade ana yi wa ma’aikata alkawarin karin albashi amma har yau bai tabbata ba. Su di kungiyar na so a maida naira 65,000 ta zama mafi karancin albashin ma’aikaci a Najeriya.