Likita ya yi kira da a rika dafa nama tubus kafin a ci don gujewa wa tsutsar ‘Tape Worm’

0

Wani likita a asibitin ‘Jikoiyi medical center’ dake Abuja mai suna Emeka Anene ya grgadi mutane da su rika dafa naman su ya dahu sosai kafin su ci.

Likitan ya ce kin yin haka kan sa a kamu da cutar tsutsan ciki da ake kira ‘Tape worm’.

A bayanan da ya yi Anene ya ce tsutsan ‘Tape Worm’na zama ne a ciki mutum ko tabba.

Ya kara da cewa dabbobi kan kamu da wannan cuta ne idan suka ciyo tsutsotsi daga ciyawa.

” Idan ba a gaggauta sama musu magani ba cutar kan yi sanadin su.” Inji likita.

” Mai dauke da wannan cuta kan yi fama da rama da yawan cin abinci saboda tsutsar na cin abincin da mutum ke ci sannan a duk lokacin da bai ci abinci ba tsutsar za ta fara cin hanjin cikin sa.

Anene ya ce alamun wannan cuta sun hada da yawan rama, yawan cin abinci, yawan jin amai, ciwon ciki da sauran su.

Ya yi kira da a tabbata ana tsaftace muhalli, da tsaftace abincin da ake ci sannan a gaggauta zuwa asibiti da zaran ba a jin dadin jiki.

Share.

game da Author