Babban alkalin jihar Kaduna Muhammadu–Lawal Bello ya bayyana cewa tsakanin 2017 zuwa 2018 an shigar da kararraki 38,336 a kotunan dake jihar.
Bello ya sanar da haka ne ranar Litini a taron bukin sabuwar shekarar alkalai da lauyoyi kan yi duk shekara.
Ya ce daga cikin kararraki 38,336 din da aka shigar, kotu ta sallami kashi 60 bisa 100 daga ciki.
” Babban kotun jihar ta saurari kararraki 3,254 daga cikin 9,679 da aka gabatar a gabanta sannan kotun Majistare ta saurari 1,730 daga cikin 3,300 daga aka gabatar a gaban ta.
” Kotun daukaka kara ta saurari kara 2,890 daga cikin 3421 da aka shigar a gaban ta sannan kotun Shari’a ta saurari kararraki 14,432 sannan ta sallami 10,548’’.
Bello ya kuma ce kotu kostomari ta saurari kararraki 4,832 daga cikin 7,515 din da aka shigar sannan ta salami sauran.
Ya kuma yi kira ga alkalai da sauran ma’aikatan kotu da su maida hankali a aikin don ganin an rage yawan kararrakin da suke gaban kotun.
Bayan haka Bello ya kuma yi kira ga kungiyar lauyoyi da Alkalai da na jihar da su ci gaba taimaka wa fannin shari’a na jihar don ganin an samu ci gaba a fannin.
A karshe shugaban kungiyar alkalai da lauyoyi na jihar Kaduna Sule Shu’aibu ya yi kira ga babban alkalin jihar Bello da ya rage yawan lokuttan da ake dauka a shari’a.
Ya kuma ce inganta albashin ma’aikatan kotu da wuraren ajiyan takardun kara da dokoki irin ta zamani zai taimaka wajen inganta aikin shari’a a jihar.