An kori wasu ‘yan sanda uku bisa laifin kai farmakin bincike gidan Dattaijo Edwin Clark da ke Abuja ba bisa umarnin aiken su ba.
‘yan sandan sun yi wa gidan dirar mikiya ne a ranar Talata, bayan sun samu labarin cewa ana kimshe muggan makamai a gidan da ke unguwar Asokoro, Abuja.
Edwin Clark dai ya musanta zargin cewa ya na boye makamai a gidan, kuma ya nemi a yi gaggawar neman afuwar sa.
Tun jiya dai Sufeto Janar na ‘yan sanda ya nemi afuwar Edwin Clark, kuma ‘yan sanda suka bada sanarwar kama wadanda su ka kai farmakin.
Clark dai ya karbi afuwar da Sufeto Janar Idris ya nema, sai dai kuma ya ce ya na tababar da za a ce wai hukuma ba ta san ‘yan sandan sun kai farmakin ba.
Kakakin ‘Yan sanda Jimoh Moshood, ya bayyana sunayen wadanda aka kora sakamakon kai farmakin sun hada da Sufeto Godwin Musa, Sufeto Sada Abubakar, Sufeto Yabo Paul, sai kuma hukunci mai tsanani ga ASP David Dominic.
Sai dai kuma karin bincike ya tabbatar da cewa Dominic zai fuskanci kora har da gurfanarwa, tabbas ganin yadda shi ma ya ke da hannu dumu-dumu cikin keta haddin Edwin Clark, zubar da kimar Najeriya da kuma take hakki da ‘yancin dan Adam da suka yi.
Sun kai farmakin ne a ranar 4 Ga Satumba, 2018.
A kan haka Sufeto Janar Idris ya amince a dakatar da Dominic daga aikin dan sanda, har zuwa lokacin da aka kammala bincike a kan sa.
Shi kuma magulmacin da ya tsegunta musu cewa Edwin Clark na boye makamai, mai suna Ismail Yakubu, wanda ya fito daga kauyen Waru da ke cikin Gundumar Apo, Abuja, tuni an gurfanar da shi a Kotun Yankin Mpape da ke Abuja, domin amsa tuhumar bayar da bayanin karya ga jami’an ‘yan sanda.
Discussion about this post