Tulin bashin dala milyan 500 daga Chana ba abin fargaba ba ne – DMO

0

Ofishi Kula da Basussuka na Kasa, DMO, ya tabbatar da cewa babu wani dalili da zai sa ‘yan Najeriya su rika kwana da fargabar yadda za a karke da tulin bashi har na dala milyan 500 da Najeriya ta ciwo daga kasar Chana kwanan nan.

Ofishin ya bayar da wannan tabbaci ne jiya Talata, a cikin wani bayani da ofishin ya raba wa manema labarai.

Ofishin na DMO ya fitar da bayanin ne ganin yadda dimbin ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa dangane da gwamnatin Buhari ta yi takakkiya zuwa Chana ta ciko cikin ta da tulin bashin da wasu ke ganin tamkar Najeriya na kokarin komawa karkashin mulkin mallakar Chana ne.

Ofishin DMO ya ce za a yi amfani da basussukan domin a cika alkawarin da aka dauka na gudanar da ayyukan gina titina, hanyoyin jiragen kasa da jiragen sama, ayyukan samar da ruwa, noma da kuma hasken lantarki.

Ofishin ya tabbatar da cewa matakan biyan bashin ba su da wani tsaurin da za a ce Najeriya ta gagari biya, ko kuma za ta gurgunce kafin ta kammala biya.

“Don haka maganar a ce kamfanonin Chana za su kwace kadarorin Najeriya idan an kasa biyan bashin, bai ma taso ba.”

Share.

game da Author