A yau Lahadi ne za a yi zaben fidda gwani na Jam’iyyar PDP a jihar Kaduna.
Wannan zabe dai kowa ya maida hankali a kai domin kuwa kusan duk manyan ‘yan siyasan Kaduna suna neman jam’iyyar ta tsaida dayan su ne dan takarar gwamnan jihar.
Cikin wadanda ake wa ganin sune kan gaba a cikin ‘yan takaran sun hada da tsohon dan majalisa Isah Ashiru wanda a zuwa yanzu an shaida mana cewa ‘yan takara uku sun janye wa.
Bayan shi akwai tsohon gwamna Ramalan Yero, Sanata Sule Hunkuyi da tsohon shugaban hukumar NEMA, Sani Sidi.